Daga Ma'aikacinmu
Sararin samaniyar Sansanin Sojin Saman Waterkloof da ke Centurion, Pretoria, Afirka ta Kudu daga ranar Larabar nan18 ga Satmba, zai fara karbar bakuncin wasanni da jiragen sama, shawagin sojoji a sama da nuna kwarewar tukun jirgi.
Hakan zai zo ne a yayinda za a fara baje-kolin kayan sufuri da tsaro na sama mai taken 'Africa Aerospace and Defence (AAD)' karo na 12.
Taron da za a kammala a ranar 22 ga Satumba, na da manufar gabatar da jiragen yaki na soji daga manyan kamfanonin tsaro da ke ciki da wajen nahiyar Afirka.
Kamfanonin kayan ayyukan soji daga Kenya, Afirka ta Kudu, Bostwana, Senegal, da Morokko a su bi sahun takwarorinsu daga wajen nahiyar wajen baje-kolin kwarewarsu.
"Wannan baje-koli karo na 12 ya zo a lokacin d aya dace, saboda ya yi daida da lokacin da Afirka ta Kudu ke cika shekaru 30 da dabbaka dimokuradiyya. Tana kuma bayyana muhimmancin hadin kai tsakanin gwamnatoci," in ji Shugabar AAD Ms segomotso Tire, a wata sanarwa da ta fitar.
Masu shirya baje-kolin sun kuma ce taron zai kunshi Shirin Cigaban Matasa (YDP) da ke kawo dubunnan matasa masu neman ilimi waje guda don su samu damarmakin zurfafa ilimi a fannin kmiyya da fasahar kere-kere, injiniyanci da lissafi.
Ana gudanar da taron duk bayan shekaru biyu a Afirka ta Kudu, inda masu shirya shi suke cewa "yana taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arzikin Afirka ta Kudu ta hanyar samun kudaden shiga daga tikitin da ake sayarwa, karbar baki, yawon bude ido da samar da ayyukan yi ga dimbin jama'a."
A 2022, baje-kolin ta samar da ayyukan yi sama da 1350, inda masu ziyara na kasa da kasa suka bayar da gudunmowar rand miliyan 135 (dala miliyan $7,678,373) ga kudaden da kasar ke samu a cikin gida.
Wani babban abu a wajen taron kuma shi ne yadda zai kara karfafa alakar da ke tsakanin kasashe musamman ma masana'antun tsaronsu da gwamnatoci, in ji masu shirya baje-kolin.