Abokan wasansa a gasar, da kuma masu sha'awar ƙwallon ƙafa da yawa, sun ci gaba da nuna goyon baya ga ɗan wasan.

Daga Charles Mgbolu

Fitattun mutane a Nijeriya sun yi Allah-wadai da cin zarafin da dan wasan Super Eagles Alex Iwobi ya fuskanta a intanet, bayan da Nijeriya ta sha kaye a wasan karshe na 2023 na AFCON a ranar Lahadi a hannun Cote d'Ivoire mai masaukin baki.

Mawaki Falz da dan wasan barkwanci AY Makun, da kuma fitaccen mai gabatar da shirye-shirye a gidan rediyon Dotun na daga cikin fitattun muranen da suka yi amfani da kafafen sadarwarsu na sada zumunta wajen kare ɗan wasan Super Eagles bayan da ya sha kakkausar suka kan rawar da ya taka a gasar ta AFCON.

"Kowane ɗan wasan da ya sanya kayan wasa mai kore da fari don wakiltar mu yana yin sadaukarwa ne mai girma, kuma bai cancanci a yi masa irin wannan cin zarafin ba.

Muna yawan magana a kan batun cin zarafi ta intanet, amma duk da haka muna gaggawar nuna adawa ga mutanenmu ta hanyar cin zarafinsu a intanet. @alexanderiwobi Muna son ka ɗan'uwa! Na gode, "in ji Falz a Instagram.

Falz ya sanya wani hoton ɗan ƙwallon a jikin saƙon da ya wallafa ɗin, inda ya rubuta "Muna yin nasara tare, muna kuma faɗuwa tare."

Shi kuma AY Makun a nasa saƙon da ya wallafa ya yi tur da cin zarafi ta intanet ne tare da yin kira ga masoyansa da su dinga girmama al'adar nuna kulawa.

"Abin takaici ne ganin yadda kuka dinga nuna halayyar cin zarafin wannan matashin wanda laifinsa a wajenku shi ne don ya je wakiltar ƙasarsa. Gobe kuma sai ku dinga mamakin dalilin da ya sa mutane irin su Saka da sauran su ba za su taɓa buga wa Nijeriya wasa ba.

"Lokaci ya yi da ya kamata tunaninku ya wuce haka, tare da yin duba kan mummunan tasirin da mugwayen halayenku za su jawo. Ya kamata mu dinga yaɗa al'adar girmama mutane a intanet tare da kare cin zarafi. Ku yi ƙoƙari ku nuna soyayya ❤️ga @alexanderiwobi a ƙasan wannan saƙon.

Shi kuwa fitaccen mai gabatar da shirye-shiryen rediyo Dotun ba Allah wadai kawai ya yi da cin zarafi ta intanet ba, har neman gafarar Iwobi sai da ya yi.

"''Wataƙila na yi baƙin ciki game da rashin nasararmu. Haka ne, amma ban yi fushi ba saboda ƴan wasan sun yi iya kokarinsu. Dirarwa @alexiwobi da aka yi da cin zarafi ba abu ne mai kyau ba, kuma ni ma ina jin muna bukatar mu koyi karbar ƙaddara ba tare da cutar da mutane ba. Idan mun sa ka ji daɗi, mun yi nadama sosai,’’ Dotun ya rubuta.

Tun lokacin da aka fara caccakar tasa a intanet sa'o'i kadan bayan kammala wasan ƙarshe, Iwobi ya fice daga duka shafukansa na sada zumunta, inda ya goge duk wani saƙo da ya wallafa a Instagram ban da guda ɗaya.

Abokan wasansa a gasar, da kuma masu sha'awar ƙwallon ƙafa da yawa, sun ci gaba da nuna goyon baya ga ɗan wasan.

''Za mu kawar da ƙiyayya. Za mu juya wannan yanayin cin zarafi ta intanet gizo zuwa ga tsananin soyayya ga Iwobi, "in ji wata magoyiya bayansa, Sophie, a shafin X.

TRT Afrika