Fireboy ya ce yanzu salon sautinsa na Afro-life ne ba Afrobeats ba. Hoto: Fireboy DML  

Daga Charles Mgbolu

A fagen wakokin Afirka, salon hybrids a sautin kiɗan Afrobeats kamar Atro-Rave, da Afro-Fusion, da kuma Afro-life suna kara samun karbuwa tare da bunƙasa musamman ganin yadda manyan taurarin mawakan Afirka suka rungumi waɗannan sabbin hanyoyin a matsayin nasu salon kiɗe-kiɗen wake.

Nau'in sautin kiɗan Afrobeats da ya sami lambar yabo da dawa, wanda ya hada sautin hip-pop da kiɗan al'adu da na High Life, sannan ya kara wa fitattun mawaka daga Nijeriya suna.

A yanzu haka Afrobeats hybrids ya samar da wani fikira wanda za a iya cewa ita ce alama mafi karfi a sauyin nau'in salon da aka samu a fagen wakoki.

A hirarraki daban-daban, taurarin mawakan Nijeriya irin su Burna Boy wanda ya lashe lambar yabo ta Grammy da Rema mai rike da lambar yabo ta kanbun ''Guinness World Awards'' da Fireboy DML wanda ya lashe lambar yabo ta wakokin Afirka, sun zama misalai na mawakan da suka ce sabon salon waken su ya sauya daga Afrobeats.

A shekarar 2015 da 2022 a yayin da Burna Boy yake tallata kundin wakokinsa mai suna 'Love, Damini', ya jaddada cewa sautinsa a matsayin 'Afrofusion'.

''Na hada sauti da salo kiɗe-kiɗe da al'adu daban-daban kana na mai da su nau'i daya wanda ake kira Afrofusion'', a cewar sanarwa da Burna Boy ya yi wa manema Labaran nishadi a Amurka.

A 2019, wani furodusan kiɗa daga Afirka ta Kudu kuma mai mawaki Toya Delazy ta gabatar da wani salon nau'in kidanta da ta kira "Afrorave," wanda ke haɗa nau'in sautin gareji da waƙoƙin Zulu.

Burna Boy ya bayyana cewa ana kiran sautinsa da Afrofusion. / Hotuna: Getty Images

Kazalika a watan Mayun shekarar 2021, Rema ya sanar da cewa zai fara kiran sautinsa da "Afrorave," wani bangare na salon waken Afrobeats inda ya hade kiɗan wakoƙin Larabawa da Indiyawa.

Sauya sunan waken na baya-bayan nan ya fito ne daga Fireboy DML, wanda ya shaidawa Black Entertainment Television (BET) cewar a wannan watan sautinsa ya sauya daga Afrobeats zuwa Afro-life.

Wannan sauyin da aka samu ya haifar da muhawara sosai daga masoya a kafafen sada zumunta wadanda suka firgita da cewa salon Afrobeats da suka sani zai sauya a gaban idanunsu.

'Rashin ratsa zuciya da kalaman wakoki'

Ko da yake Fireboy DML, ya ba da dalilansa na canza sunan salon sautinsa, yana mai cewa: "kafin na shigo, salon Afrobeats yana da kyau.

"An gina shi a kan tsarin wakoki masu ratsa zuciya da armashi da kuma harsashi, da kuma salon kayan kidansa daban ne. Sai na fahimci cewa akwai wani abu da ya rasa, kuma wannan ya kasance salon tsarkakakken ruhi a yanayin wakokinmu da kiɗan mu.

''Abin da na shigo da shi ke nan. Kuma na ga idan kuna kawo sabon abu a teburin, yana buƙatar sabon suna. Shi ya sa na kira shi Afro-Life-Afrobeats wanda ya kasance yana da tunani mai zurfi cikinsa.

Kalmominsa sun yi daidai da tunanin Burna Boy, wanda, a cikin wata hira, da ya yi da Apple Music a watan Agusta 2023 gabanin fitar da kundin wakokinsa na bakwai, 'I Told Them' ya bayyana cewa salon nau'in Afrobeats na "rashin tunani mai zurfin."

Burna Boy ya bayar da hujjar cewa sautin Afrobeats ya kamata ya wuce tambayar magoya baya don jin daɗi saboda ba shi ne ainihin wakilcin rayuwa ba, wanda ko yaushe yana gabatar da lokuta masu kyau da mara kyau.

Rema ya ce ana kira sautinsa da Afrorave. Hoto: Reuters

"A ƙarshen dai, rayuwa ba lokaci ba ce mai ban mamaki, komai kyawun lokacin da kuke da shi yanzu, ko kuma kuna da wani lokaci, ko kuna shirin samun, har yanzu za ku fuskanci rayuwa.

"A gare ni, ina jin kamar kiɗa ya kamata ya zama ainihin mawallafi kuma mai zane shi ne mutumin da ke da kwanaki masu kyau, ranaku marasa kyau, manyan ranaku, da mafi munin ranaku," in ji Burna a cikin shirin bidiyo na Apple da aka wallafa a shafin X.

Burna ya sha suka sosai saboda kalamansa daga magoya bayansa da yawa waɗanda suka zarge shi da sanya sunan baƙar fata da ya bunkasa kidan sa da tambarin sa. Amma an riga an shuka iri na tunani, tare da wasu masu fasaha yanzu suna sake tunani.

Mawaƙa irin su Rema, sun yi kira ga taurarin mawaƙa da kada su ƙi waƙoƙin Afrobeats, sun ƙara da cewa ya canza sunan sautinsa ne kawai saboda yana so ya canza sautin Afirka.

TRT Afrika