Akwai manyan masu fada-a-ji a Facebook da suka halarci taron /Hoto: Kano Facebook Connect Committee

Watakila mutane da dama suna kallon shafukan sada zumunta irin su Facebook a matsayin wajen sharholiya da musu da kuma debe kewa ne kawai.

Ga alama ba a nan abin ya tsaya ba, don akwai wasu abubuwan ayyuka masu amfani da shafin suka bijiro da su don ci gaban al’umma.

A baya-bayan masu fada-a-ji a dandalin Facebook a arewacin Nijeriya sun bijiro ko kirkiro da wata aniya ta son ganin sun ciyar da mu’amalar wannan saha gaba.

Salon da suka bullo da shi din shi ne gabatar da taro na masu ruwa-da-tsaki a dandalin da suka hada da masu fada-a-ji da mabiyansu, wanda aka yi wa take da Facebook Connect.

Jihohi irin su Kano da Filato da Katsina da Jigawa da Bauchi da Kaduna duk sun shirya irin wannan taro, a yayin da a hannu guda kuma ake ta shirye-shiryen gudanar da gagarumin taron da ake sa ran zai hada dukkan masu fada-a-ji na Facebook na arewacin Nijeriya, mai taken Arewa Facebook Connect.

An gudanar da taron Kano Facebook Connect ranar Litinin 24 ga watan Afrilu, kuma sakataren shirye-shirye na kwamitin, Mukhtar Idris Bature Mai Salati ya shaida wa TRT Afrika cewa an gabatar da makaloli a wajen.

Mahalarta irin su Barista Abba Hikima Fagge sun yi bayani kan yadda za a kauce wa aikata laifuka a soshiyal midiya /Hoto: Kano Facebook Connect

Ga wasu muhimman abubuwa da taron ya mayar da hankali a kansu:

1. Sada Zumunci

Kwamitin shirya taron ya ce babban makasudin yin sa shi ne don a sada zumunci a ga juna a yi wa juna fatan alheri tare da daukar hotuna.

"Kuma ga alama kwalliya ta biya kudin sabulu don an taru kuma an gaisa an yi hotuna an ci an yi hani'an," in ji sakataren.

2. Wayar da kai kan kaucewa laifuka a soshiya midiya

Wani batu na biyu da aka tattauna a wajen wannan taro shi ne wayar wa mahalartansa kai kan yadda za su kauce wa aikata laifukan da ka iya jawo musu tuhumar hukumomi.

“Fitaccen mai amfani da Facebook kuma lauya, Barista Abba Hikima ya yi bayani kan yadda mutum zai kauce wa yin laifin da zai fada komar jami’an tsaro.

Akwai mata masu fada-a-ji  a Facebook da dama da suka halarci taron /Hoto: Kano Facebook Connect

“Irin wadannan laifuka sun hada da yin sojan gona da sunan wani ana yada sakonnin da ba su da ce ba, da bata wa mutum suna, da amfani da hoton yara a yanayin da ka iya sa rayuwarsu a hatsari da kuma wallafa abin da ya shafi tsiraicin wasu,” in ji Mai Salati.

3. Wane ne dan soshiyal midiya?

Bello Muhammad Sharada shi ne ya gabatar da makala a kan "wane ne dan soshiyal midiya, da rawar da ya kamata ya taka, da kuma rabe-raben ‘yan soshiyal midiya."

Wannan makala ta yi duba ne kan abin da ya kamata masu amfani da shafin, musamman masu dumbin mabiya su yi don amfanar da al’ummar da ke bibiyar su.

Mai Salati ya ce wannan babi ya tabo bangarori da suka hada da masu fada-a-ji a soshyal midiya da ke yawan magana a kan ko dai siyasa ko barkwanci ko kasuwanci ko ilimi ko addini kuma ma al’amuran yau da kullum da irin tasirin ayyukansu a dandalin.

4. Taimaka wa hukumomin tsaro

Cikin mahalarta taron har da jami’an hukumomin tsaro, kamar mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda shi ma ya gabatar da makala.

Wakilan hukumomin tsaro irin su DSP Abdullahi Haruna Kiyawa (na tsakiya) na rundunar 'yan sandan Jihar Kano ma sun halarci taron /Hoto: Kano Facebook Connect

Makalar tasa ta yi duba ne a kan yadda ‘yan soshiyal midiya za su taimaki jami’an tsaro don samar da zaman lafiya da taimaka wa da dabarun dakile aikata laifuka a cikin al’umma.

5. Zagi da cin zarafi a soshiyal midiya

Shi kuwa fitaccen dan jarida a Jihar Kano, Nasiru Salisu Zango, ya yi magana ne a kan cin zarafi da zagin mutane da ke neman zama ruwan-dare a dandalin.

Ya nuna takaicinsa kan yadda a lokuta da dama idan mutum ya bayyana ra’ayinsa kan wani batu sai mabiya su yi masa caa da zagi da cin mutunci.

Mahalarta na fatan taro irin wannan zai iya yin tasiri wajen rage wannan mummunar dabi’a, ta hanyar fito da matakan da za a hana zagin mutane ba dalili, kuma da yadda za a kiyaye hakan.

6. Mutunta bambance-bambance

Ana fatan taron ya kawo sauyi mai kyau da ci gaba a yadda ake amfani da Facebook /Hoto: Kano Facebook Connect

Wani maudu’i da taron ya duba shi ne na yadda za a rage nuna bambancin ra’ayin siyasa a dinga siyasa ba da gaba ba, kamar yadda Mai Salati ya fada.

Ya kara da cewa ba bambanci siyasa ba kawai, ana so taron ya yi tasiri wajen rage nuna bambanci a bangarori da dama.

Malaharta taron

Taron dai ya samu mahalata sama da 400 a cewar kwamitin. Kuma an yi wa mutane rijistar halarta ne a kan naira dubu uku.

Wasu mahalarta taron /Hoto: Kano Facebook Connect

Daga cikin manyan masu fada-a-ji na dandalin Facebook na Kano da suka halarci taron akwai irin su:

  • Yakubu Musa
  • Sanusi Musa SAN
  • Malam Kabiru Sufi
  • Nasiru Zango
  • Abba Hikima
  • Ibrahim Musa
  • Aliyu Dahiru Aliyu
  • Sheriff Almuhajir
  • Kabiru Dakata
  • Ambasada Auwal Dan Larabawa
  • DSP Adullahi Kiyawa
  • Na ‘Yar Talla
  • Salisu Yahaya Hotoro
  • Hauwa’u Faruk
  • Nadiya Ibrahim Fagge

Wasu manyan masu fada-a-ji da ba su samu halarta ba kuma kamar su Abdulaziz Abdulaziz da Zainab Naseer sun wallafa sakonnin ban hakuri, tare da fadar uzurorin da suka hana a gan su a wajen.

Sama da mutum 400 aka yi wa rijista kuma suka halarci taron jin kwamitib /Hoto: Kano Facebook Connect

A yanzu za a iya cewa hankula sun karkata wajen ganin yadda za ta kaya a babban taron na Arewa Facebook Connec, wanda ba a kai ga sanya ranar yin sa ba, kamar yadda shugaban kwamitinsa Dakta Sheriff Almuhajir ya shaida wa TRT Afrika.

"Amma dai tabbas a yankin arewacin Nijeriya za mu gudanar da shi," in ji Dakta Almuhajir.

TRT Afrika