Fitacciyar ‘yar fim din Kannywood Hajiya Saratu Gidado da aka fi sani da Daso ta ce a yanzu ta fi mayar da hankalinta kan abubuwan da suka shafi jinƙai a tsakanin al’umma.
Daso, wadda ta ce duk da cewa har yanzu ba ta daina yin fina-finai ba musamman masu dogon zango da aka fi nunawa a kafar Youtube, ta shaida wa TRt Afrika Hausa cewa ta shiga ayyukan jinƙai ne ka’in da na’in saboda ganin “halin ha’ula’in da ƙasa da al’umma ke ciki na wahala.”
Ta ce ta fara ayyukan da suka shafi raba abinci dafaffe da ɗanye da kayan sakawa musamman na sanyi a lokacin hunturu da magunguna ga marasa lafiya daga cikin irin rufin asirin da take samu a harkar sana’arta ta fim.
“Saboda halin rayuwa da muke ciki, ba ma kasar nan kadai ba, duk duniya don muna magana da wadanda ke wasu kasashen, cewar rayuwa ta yi tsanani, samun abinci na wuya, to balle nan bangarenmu kuma a arewacin Nijeriya, ana fama da matsalar rashin abinci.
“Wannan dalilin ya sa na shiga harkar nan. Nake bi unguwannin marasa galihu da ƙauyuka don taimaka wa mutane da ɗan abin da Allah ya hore min.
“Abin da nake yi shi ne ina dafa abinci duk ranar Juma’a kamar shinkafa fara da mai da yaji saboda a halin da ake ciki ba ni da halin sayen kayan miya, a hakan ba da yawa ba ne amma mutane da dama suna samu su ci.
“Sannan a lokacin sanyi muna rabawa yara rigunan sanyi sadaka, haka muka sayo kayan gwanjo masu kyau muka raraba musu a wannan sanyin da ake yi. Har kan titi muke bi irin masu kwana a wajen ɗinnan mu ba su barguna.
Sai dai Daso ta ce dambu idan ya yi yawa ba ya jin mai, sai da ta kai da tana neman tallafin masu hali don su shiga cikin wannan harka ta jinƙai da taimakon mutane ta hanyar bayar da abin da Allah ya hore musu.
“Amma duk da haka ba mu cika samun tallafin ba sai dai ɗan kaɗan da ba a rasawa, amma hakan ba zai sa na daina aniyata da nake kai ba,” ta faɗa.
Hajiya Saratu ta kuma mayar da martani a kan masu ganin ta yi girma da wallafa bidiyo a shafin Tiktok, inda ta ce tana da shafi a duka sauran hanyoyin sada zumunta irin su Facebook da Instagram da X, kuma tana da dumbin mabiya a kansu, don haka ba ta ge wani bambaci tsakanin su da Tiktok ba da har mutane za su dinga ganin aibinta don tana amfani da Tiktok.
“Abubuwan da nake wallafa duk na barkwanci ne da ilimantarwa ba wasu abubuwa ne na kunya ba da za a ce me ya sa na yi,” ta fada.