A Tribe Called Judah: Wadda ta shirya fim din da ya samu naira biliyan daya cikin kwana 21

A Tribe Called Judah: Wadda ta shirya fim din da ya samu naira biliyan daya cikin kwana 21

Fim din na 'A tribe Called Judah' ya samu yabo daga ciki da wajen Nijeriya.
Fim din na 'A Tribe Called Juda' labarin wata mata ce wadda ko wanne daga cikin yaranta biyar na da uba daban:Hoto/Funke Akindele

Wani sabon fim din Nijeriya wanda ya kafa tarihi a matsayin fim din ya samu naira biliyan daya a sinima aikin wata 'yar fim da ta sha kaye ne a zaben gwamnan Legas kimanin shekara daya da ta wuce.

Funke Akindele ce mataimakiyar dan takarar gwamnan jam'iyyar PDP a jihar, Olajide Adediran, a zaben da aka yi a watan Maris na 2023.

Funke da dan takarar su ne suka zo na uku a zaben 2023, amma 'yar fim din ta ce lamarin ya koya mata darasi kuma ba ta yi da-na-sanin tsayawa takara ba.

Kwatsam a watan Janairun 2024 sai fim dinta mai suna 'A Tribe called Judah' ya kafa tarihi bayan ya samu fiye da naira biliyan daya cikin kwanaki 21 bayan an fara nuna shi a sinima a fadin Nijeriya.

“Ga kasata Nijeriya mai daraja, wannan tabbaci ne cewa dukkanmu masu nasara ne a duk inda muke,” in ji Akindele a wani bidiyon da ta wallafa a shafinta na Instagram.

Nasarar da ta samu ta dara tarihin da ta kafa a baya da fina-finanta: 'Battle on Bukka Street' (da ya samu N668.4m) da kuma 'Omo Ghetto' (da ya samu N636.1m).

Yabo

Ta sha yabo daga Shugaba Bola Tinubu da kuma wasu manya a kasar. Sun shaida kokarinta a matsayin daya daga cikin sabbin masu ba da labari da ke nishadantar da 'yan Afirka.

“Shugaba Tinubu ya taya Funke Akindele murna kan fim dinta da ya kafa tarihi tare da taya ta murna kan gudunmawarta kan ci-gaban masana'antar fim,” a cewar wata sanarwa daga fadar shugaban kasar.

“Na yaba wa 'yan Nijeriya kan yadda suke tallafa wa kokarin kirkirar abubuwa na gida. Za mu samar da yanayi da zai sa masana'antar ta habaka,” in ji sanarwar.

Dan takarar jam'iyyar da ke adawa ta PDP a zaben 2023 Atiku Abubakar ya ce fim din “wata alama ce ta alfaharin al'adar kasar da kuma halayyar jajircewa ta masana'antar Nollywood."

"A Tribe Called Judah ba fin ba ne kawai, abin al'ada ne mai daraja wanda yake nuna tagomashi da juriyar sinima a Nijeriya," in ji shi.

Shi ma dan hamayya na jam'iyyar LP, Peter Obi, ya taya Akindele murna kan nasararta, inda ya ce masana'antar Nollywood ta kasance daya daga cikin ababe mafi yawa da kasar ke alfahari da su a kasashen waje.

Ya karfafa wa masu shirya fina-finai gwiwa su ci gaba da ba da labarai da ke goyon bayan gaskiya da kuma aiki tsakanin 'yan Nijeriya.

A Tribe Called Judah ya samu yabo a ciki da wajen kasar. Labari ne na wata mata mai yara biyar.

Mafarin shahara

Akindele ta fara shahara ne a lokacin da take fina-finan Yarbanci inda ta yi fim din Jenifa a shekarar 2008.

Fim din Jenifa ya sa ta samu lambobin yabo tare da fito da ita a masana'antar Nollywood. Bayan wannan ne ta yi wani shahararren fim, Omo Ghetto, wanda shi ma ya kara mata daukaka.

Daga baya ta mayar da labarin barkwancin Jenifa fim mai dogon zango kuma ta kara tsawaita labarin Omo Ghetto (‘Omo Ghetto: the Saga’).

TRT Afrika