| Hausa
NIJERIYA
5 minti karatu
Tinubu ya kare matakin karɓo bashi daga waje, ya ce Nijeriya na buƙatar haɓaka tattalin arziki
Kalaman shugaban ƙasar na zuwa ne a cikin sukar matakin gwamnatin na aron kuɗaɗe da kuma tasirin hakan ga nauyin bashi kan ƙasar.
Tinubu ya kare matakin karɓo bashi daga waje, ya ce Nijeriya na buƙatar haɓaka tattalin arziki
Shugaba Tinubu ya ce Nijeriya na buƙatar kuɗin don inganta ababen more rayuwa da za su samar da tattalin arziki da kimarsa ta kai dala tiriliyan ɗaya

Shugaba Bola Tinubu ya kare matakin gwamnatinsa na karɓo bashi daga hukumomin ƙasa da ƙasa da bankuna, yana mai cewa Nijeriya na buƙatar zuba jari mai ɗorewa kan ababen more rayuwa domin cim ma burinta na samar da tattalin arziki da ƙimarsa ta kai dala tiriliyan 1 nan da shekarar 2030.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, kakakin shugaban Nijeriya, Bayo Onanuga, ya ce Tinubu ya yi waɗannan kalaman ne a cikin wata maƙala mai taken ‘daga gyara zuwa samar da sakamako: Zuba jarinmu a ababen more rayuwa da ci-gaba’.

Kalaman shugaban na zuwa ne sakamakon sukar da yake sha daga wurin ‘yan adawa cewa gwamnatinsa na karɓo bashi ba tare da aiwatar da ayyukan da suka dace ba, matakin da suka ce zai ƙaƙaba wa ƙasar nauyin bashi.

Tinubu ya ce ya kamata a mayar da hankali kan fa’idar da aka samar daga kuɗaɗen da aka karɓo maimakon adadin bashin da aka ci.

“Sahihiyar tambayar ita ce: ba wai nawa muka karɓo ba, amma abin da muka gina da kuma makomar da muka bari a baya,” in ji Tinubu.

Ya bayyan babbar hanyar bakin teku ta Legas zuwa Calabar da babbar hanyar Sokoto zuwa Badagry da babbar hanyar Sahara da inganta layukan lantarki da zamanantar da muhimman tashoshin jiragen ruwa a Legas a matsayin muhimman ayyuka da ake tsammanin za su ƙarfafa ikon iya samar da ci-gaba a Nijeriya.

Tinubu ya ce ana tsammanin babbar hanyar bakin tekun Legas zuwa Calabar ta rage kuɗin jigilar kayayyaki a yankin da kashi 15 zuwa 20 cikin 100 kuma za ta iya ba da gudunmawa ta kashi biyu cikin ɗari ga ƙimar tattalin arziki ta hanyar faɗaɗa cinikayya da yawon buɗe ido da ayyukan masana’antu.

Ya ƙara da cewa an yi ƙiyasin cewa aikin zai samar da ayyuka 100,000 kai-tsaye a fannin gine-gine da aikin injiya, tare da wasu ayyuka fiye da 150,000 a harkar jigila da samar da kayayyaki da ayyuka masu alaƙa.

“Ba wai kawai muna gine manyan hanyoyi ba ne. Muna buɗe yankunan tattalin arziki da haɗa kan kasuwanni da buɗe ƙofofi wa masana’antu da kuma sake fasalin yankunan tattalin arzikin Nijeriya,” in ji shi.

“Ba za mu iya gina tattalin arziki mai ƙimar dala biliyan 1 ba da ababen more rayuwa da aka tsara domin wani tattalin arziki da bai wuce wani ɓangare kaɗan na ƙimarsa ba,” a cewar Tinubu.

Shugaban na Nijeriya ya alaƙanta alƙaluman muhimman ci-gaban tattalin arzikin da aka samu ga gyare-gyaren da aka gabatar daga watan Mayun shekarar 2023, ciki har da cire tallafin man fetur da haɗa farashin kasuwar kuɗaɗen ƙetare wuri ɗaya da gyare-gyaren dokar haraji da matakan daƙile hauhawar farashi.

Masu AlakaTRT Afrika - Nijeriya ta amince da biyan ma’aikatan gwamnatin tarayya naira 70,000 kudin sufuri duk wata

Ya ce haɓakar ƙimar tattalin arzikin ƙasar ya kai kashi 4.43 cikin 100 a rubu’i na biyu na shekarar 2026, yayin da hauhawar farashi ta faɗi zuwa kashi 14.63 cikin 100 a watan Satumba daga kashi 20.98 cikin 100 a shekarar da ta gabata.

Shugaban ya kuma ce jumullar kuɗaɗen ajiyar ƙetare na ƙasar sun ƙaru zuwa dala biliyan 55.1 a ranar 9 ga watan Oktoban 2026, ciki har da kimanin dala biliyan 46 na kuɗaɗen ajiya mafi ƙanƙanta, yayin da yawan haraji idan aka kwatanta da yawan ƙimar tattalin arziki ya ƙaru zuwa kashi 12.5 cikin 100 daga kashi bakwai.

Tinubu ya ce gyare-gyaren sun taimaka wajen mayar da daidaito na tattalin arzikin ƙasa baki ɗaya da ƙarfafa harkar kuɗin gwamnati da kuma inganta matsayar Nijeriya a kasuwannin kuɗi na ƙasa da ƙasa.

“Matakan da aka da aka ɗauka tun shekarar 2023 suna da wuya, amma sun zama dole,” in ji Tinubu.

Shugaban ya nuna kallo mai kyau da kamfanonin ƙasa da ƙasa masu auna amincin bashi ke yi wa ƙasar a matsayin hujja na ingancin gwarin gwiwar masu zuba jari.

“Waɗannan ba nuna goyon baya na siyasa ba ne; ƙimantawa ne mai ‘yanci da kamfanonin duniya da masu sa ido da masu zuba jari da ke duba ƙima suka yi inda suka ga kuɗin ajiyar ƙetare mai ƙarfi da ingancin tafiyar da tattalin arzikin ƙasa da ƙarin yarda da harkar kuɗi,” in ji Tinubu.

Ya ce ingancin matsayin zai iya taimaka wa Nijeriya janyo haɗin kan kamfanonin da ƙasashe masu zuba jari da samar da samar da kuɗi na lokaci mai tsawo da kuma rage tsadar bashi.

Tinubu ya ƙara da cewa gwamnatinsa tana matsa bashi daga samar da kuɗi wa matsin kuɗin mai gajeren lokaci zuwa zuba jari da za su iya samar da riba na tattalin arziki da samar da ayyukan yi da faɗaɗa damarmaki ga masu zubawa a shekaru na gaba.

Ya ce gwamnatin tana kuma bin tsare-tsare na bashi mai dogon zango da zai dace da iya rayuwar ababen more rayuwa da rage matsin kuɗin da kuma samar da ƙarin kuɗi mai sauƙi don zuba jari mai inganci.

Shugabna ya bayyana ababe biyar da gwamnatin tarayyar za ta mayar da hankali a kan a mataki na gaba kamar haka: sauƙin abinci da ɗorewar farashin makamashi da daidaita kasafin kuɗi da ladabi wajen kashe kuɗi da ƙarasa ayyuka da suka fi tasiri da inganta manufofi na tattalin arziki da ingancin dokoki da kuma tallafi wa iyalai tare da zuba jari a inganta ƙarewar mutane.