| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
An kama mutum biyar kan harbin bindiga ba bisa ƙa’ida ba da 'ya kashe' yarinya Maiduguri a Nijeriya
Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 2:00 na rana a ranar Asabar 4 ga Afrilun 2026, inda wasu jami’an tsaro na sa-kai da ke yin rakiya ga wani shugaban ƙaramar hukuma suka riƙa harbi sama yayin wani bikin aure a rukunin gidajen malamai na Umaru Musa Yar’
An kama mutum biyar kan harbin bindiga ba bisa ƙa’ida ba da 'ya kashe' yarinya Maiduguri a Nijeriya
An kama mutum biyar kan harbin bindiga ba bisa ƙa’ida ba da 'ya kashe' yarinya Maiduguri a Nijeriya / Others
 

Dakarun Operation HADIN KAI sun kama mutum biyar da ake zargi da hannu a harbin bindiga ba bisa ka’ida ba wanda ya yi sanadin mutuwar wata ƙaramar yarinya a yankin Ngomari, a wajen birnin Maiduguri na Jihar Bornon Nijeriya.

Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 2:00 na rana a ranar Asabar 4 ga Afrilun 2026, inda wasu jami’an tsaro na sa-kai da ke yin rakiya ga wani shugaban ƙaramar hukuma suka riƙa harbi sama yayin wani bikin aure a rukunin gidajen malamai na Umaru Musa Yar’Adua.

Rahotanni sun bayyana cewa harbin ya jawo aka samu suɓutar hannu inda harasashi ya kauce ya samu wata yarinya ta kuma mutu take, lamarin da ya jawo damuwa a tsakanin al’umma.

A wata sanarwa daga bakin Laftanar Kanar Sani Uba, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Gabas a ranar Litinin, ta ce cikin gaggawa, dakarun Operation HADIN KAI tare da haɗin gwiwar Civilian Joint Task Force sun bi sawun waɗanda ake zargi tare da kama su.

Ta ƙara da cewa a halin yanzu waɗannan mutane suna tsare a hannun sojoji, kuma za a miƙa su ga hukumomin da suka dace domin ci gaba da bincike da gurfanar da su a gaban kotu bisa tanadin doka.

Hedikwatar rundunar ta yi Allah-wadai da wannan aiki, tana mai bayyana shi a matsayin rashin ƙwarewa da kuma karya dokokin amfani da makamai.

Ta jaddada cewa ƙungiyar Civilian Joint Task Force na aiki ne kawai a matsayin masu taimako, kuma ba su da izinin yin amfani da makamai ba bisa ƙa’ida ba, musamman a cikin unguwannin jama’a.

Hukumomi sun kuma fara cikakken bincike tare da haɗin gwiwar gwamnatin Jihar Borno domin gano cikakkun bayanai kan lamarin tare da tabbatar da cewa an hukunta duk masu laifi.

Duk da cewa an ce zaman lafiya ya dawo a yankin, dakarun tsaro sun ƙara tsaurara matakan sa ido domin tabbatar da doka da oda.

Rundunar ta kuma miƙa ta’aziyya ga iyalan yarinyar da ta rasu, tare da jaddada ƙudirinta na kare rayukan fararen-hula da tabbatar da adalci.

Rumbun Labarai
ADC ta shigar da kara mai hujjoji 17 a kan INEC kan soke takarar Atiku ta 2027
Jami’an Kwastam na Nijeriya sun kai ziyarar aiki Nijar don ƙarin ilimi kan dabarun tsaro
Jonathan ya yi gargaɗi kan rikicin ƙabilanci da rashin haƙuri a siyasa gabanin zaɓen 2027 a Nijeriya
Nijeriya ta kama mutum takwas bisa zargin safarar hodar iblis zuwa Turai ta Hamadar Sahara
Nijeriya na dab da samar da ‘yansandan jiha yayin da majalisun jihohi 36 suka amince da shirin
Hukumar hana safarar mutane ta Nijeriya ta bankaɗo yunƙurin safarar mutane 1,508
Tinubu ya yi wa mutum 78 afuwa bayan kama su da laifin kai hari ga ayarin motocinsa a Abuja
Majalisar yaƙin neman zaɓen APC ta ƙaddamar da shirin samar da tsaro na Tinubu na shekaru biyar
Sojojin Nijeriya sun kashe 'yanta'adda takwas, sun kuɓutar da mutum 125 da aka yi garkuwa da su
‘Yanbindiga sun kashe wani babban mai bai wa gwamna shawara a Zamfara
Faɗa tsakanin 'yanbindiga da 'yan sa-kai ya yi ajalin mutum fiye da 50 Jihar Zamfara ta Nijeriya
Jihar Katsina ta kaddamar da jami'an kula da gandun daji fiye da 1,000 domin magance matsalar tsaro
INEC ta saka ranar 28 ga Nuwamba domin gudanar da zaben gwaji gabanin zaben Nijeriya na 2027
Atiku ya buƙaci Tinubu ya yi bayani kan matakan da yake ɗauka na kawo ƙarshen kashe-kashe a Nijeriya
Jami'an DSS a Nijeriya sun kama makamai da ake zargi an shiga da su Jihar Sokoto daga Nijar
Tinubu ya bai wa ’yanwasan Nijeriya mata 'yan 17 naira miliyan ɗari-ɗari kan cin Kofin Duniya
Kyari ya musanta asarar naira tiriliyan 210 na NNPC a ƙarƙashin jagorancinsa
Rikicin Nijeriya ya tilasta wa dubban mutane tserewa zuwa Nijar: Majalisar Ɗinkin Duniya
An kashe mutum 418, an sace 227 a cikin wata biyu a Nijeriya, in ji rundunar 'yansandan ƙasar
Nijeriya za ta fara yi wa ’yan ƙasar masu digirin ƙasashen waje jarrabawa don kawar da digirin bogi