Gwamnatin Amurka ta ɗauki matakin da watakila hatta manyan masu sukar Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) ba su taɓa tunanin za ta iya ɗauka ba.
A watan da ya gabata, Washington ta sanya kotun kanta cikin jerin hukumomin da ta kakaba wa takunkumi, lamarin da ya faɗaɗa matakin da ta riga ta ɗauka kan jami'an kotun guda 13. Turai ta yi Allah-wadai da matakin. Sai dai tambayar ita ce, ko za ta ɗauki wani mataki fiye da hakan?
Saɓanin da ake samu a yanzu ya shafi binciken da ICC ke yi kan zargin aikata laifuka a Gaza, da kuma sammacin kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da tsohon Ministan Tsaron ƙasar Yoav Gallant da kotun ta bayar a watan Nuwamban 2024.
Amurka ta kuma nuna rashin amincewa da binciken da kotun ke yi kan zargin aikata laifuka da jami'an sojinta suka yi a Afghanistan.
Amurka na hujjar cewa ICC ba ta da ikon gurfanar da 'yan ƙasashen da ba su amince da huruminta ba.
Sai dai sashe na 12 na Yarjejeniyar Rome da ta kafa kotun ya bai wa ICC ikon bincikar laifukan da aka aikata a cikin ƙasar da ta amince da huruminta, ba tare da la'akari da ƙasar da wanda ake zargi ya fito ba.
Falasɗinu na cikin ƙasashen da suka amince da yarjejeniyar. Don haka, akwai saɓanin fahimta ta fuskar doka a nan, amma bai kamata a hukunta alkalai saboda gudanar da shari'ar da aka gabatar musu ba.
Alkaliyar ICC, Kimberly Prost, ta bayyana yadda takunkumin Amurka ya sa aka soke katunan bashinta, da asusun sayayya na Amazon da Google, lamarin da ya jefa ta cikin wahala wajen gudanar da wasu al'amuran yau da kullum.
Irin waɗannan matakai ba wai kawai suna jefa jami'an shari'a cikin takura ba ne, suna kuma tilasta wa bankuna da kamfanonin fasaha shiga wani yunƙuri da ka iya ware waɗannan mutane daga muhimman ayyuka.
Idan alkalai suka rasa damar gudanar da harkokin kuɗaɗensu saboda shari'o'in da suke yi, to kuwa an yi wa 'yancin cin gashin kai na bangaren shari'a babban lahani.
Matakin sanya ICC cikin jerin hukumomin da aka kakaba wa takunkumi a ranar 9 ga Oktoba yana da irin wannan barazana ga kotun baki ɗaya.
Gabaɗaya, an haramta wa 'yan ƙasa da kamfanonin Amurka mu'amala da mutanen da aka sanya wa takunkumi, yayin da za a iya ƙwace ko daskarar da kadarorin da ke ƙarƙashin ikon Amurka.
Sai dai Washington ta bayar da wasu lasisi da ke ba da damar ci gaba da gudanar da yawancin ayyukan yau da kullum na ICC har zuwa ranar 7 ga Afrilu, 2027, tare da wasu keɓancewa da suka shafi wasu hidimomi.
Wannan izinin na ɗan lokaci ba ya nufin cewa kotun tana da cikakken tsaro. Yana nufin cewa dole ne wata kotun ƙasa da ƙasa ta riƙa tsara harkokin kuɗaɗenta, kwangilolinta da fasahohinta bisa wa'adin da kuma keɓancewar da wata gwamnati mai adawa da aikinta ta gindaya.
Turai ta fito ta yi magana, amma shin za ta ɗauki mataki?
Martanin Turai ya kasance mai ƙarfi a kalamai, amma ba tare da cikakken ƙwazo wajen ɗaukar mataki ba. Shugabannin ƙasashen Turai sun bayyana goyon bayansu ga kotun a taronsu na ranakun 15 da 16 ga Oktoba, tare da buƙatar Washington ta janye matakinta.
A ranar 23 ga Oktoba, Hukumar Tarayyar Turai ta shawarci kamfanonin ƙasashen EU da su ci gaba da samar da hidimomi ga ICC, inda ta yi nuni musamman da tsarin biyan kuɗi na Turai.
Sai dai har yanzu hukumar ta fi karkata ga amfani da diflomasiyya, ba ta kuma fara amfani da babbar dokar da ke hannunta domin dakile tasirin takunkumin Amurka a wajen ƙasarta ba.
Alƙawarin nuna goyon baya ba zai yi tasiri sosai ba idan bankuna da kamfanonin fasaha da ake buƙatar su samar wa kotun hidimomi suna ci gaba da fargabar ramuwar gayyar Amurka.
Wannan jinkiri ya fi wuya a fahimta idan aka yi la'akari da cewa dukkan ƙasashe 27 na Tarayyar Turai sun amince da Yarjejeniyar Rome.
A ƙarƙashin sashe na 86 na yarjejeniyar, ƙasashen sun ɗauki alhakin ba da cikakken haɗin kai ga kotun wajen bincike da gurfanar da mutanen da ake zargi da aikata laifukan da ke ƙarƙashin huruminta.
Wannan sashe bai tilasta wa ƙasashen fara amfani da dokar hana bin takunkumin ƙasashen waje kai tsaye ba, amma yana nuna cewa batun ya wuce maganganun diflomasiyya, domin yana da alaƙa da wajibcin da suka ɗauka a ƙarƙashin yarjejeniyar.
Ƙasashen da suka ɗauki alhakin tallafa wa kotun ta hanyar yarjejeniya ba za su iya ɗaukar lalacewar 'yancin gudanar da aikinta a matsayin matsalar wasu kawai ba.
Wannan dokar ita ce Blocking Statute ta Tarayyar Turai, wato Dokar Majalisar Tarayyar Turai mai lamba 2271/96.
An ƙirƙire ta ne a shekarar 1996, sakamakon matakan Amurka da suka shafi Cuba, Iran da Libya. Babban abin da dokar ke ƙunshe da shi shi ne cewa Washington ba za ta ɗauka cewa takunkumin da ta kakaba wa wata ƙasa ko hukuma dole ne ya zama abin da zai jagoranci harkokin kasuwanci na halal a Turai ba.
Dokar ba wai kawai wata sanarwar nuna goyon baya ba ce. Tana ƙunshe da wajibai da aka tsara domin hana kamfanonin Turai zama kayan aikin wata gwamnatin ƙasashen waje wajen aiwatar da manufofinta na takunkumi a wajen ƙasarta.
A duk lokacin da aka sanya wasu takunkuman Amurka cikin jerin ƙarin bayanan dokar, ana hana kamfanonin Turai bin waɗannan matakai, sai dai idan an ba su izinin musamman.
Kamfanonin da abin ya shafa na iya neman diyya kan asarar da suka yi sakamakon aiwatar da waɗannan takunkumai. Haka kuma, ba za a iya aiwatar da hukuncin wata kotun ƙasar waje da aka yanke bisa waɗannan takunkumai a cikin Tarayyar Turai ba.
Haka kuma, kamfanonin da abin ya shafa suna da wajibcin kai rahoto kan lamarin.
Hukumar Tarayyar Turai ce za ta yi gyara ga ƙarin bayanan dokar domin ta shafi takunkumin da aka kakaba wa ICC. Dokar da ake da ita a yanzu ba ta kare kotun kai tsaye. Wannan shi ne matakin da Turai ta yi ta jan ƙafa wajen ɗauka.
Bankin ABN AMRO na ƙasar Netherlands, wanda ke kula da harkokin kuɗaɗen ICC, na fuskantar barazanar fuskantar hukunci daga Amurka idan ya ci gaba da samar wa kotun hidimomin banki bayan karewar wa'adin izinin wucin-gadin da Amurka ta bayar a watan Afrilun 2027.
Yawan ayyukan da bankin ke gudanarwa a Amurka na jefa shi cikin babban haɗari ta fuskar kuɗi da dokokin harkokin banki.
Ko da yake bankin bai sanar da cewa zai yanke hulɗarsa da kotun ba, rashin tabbas kan makomarsa yana ƙara jefa shi cikin mawuyacin hali.
Amfani da dokar Blocking Statute ta EU zai iya hana bankin janye hidimominsa ga ICC kawai domin bin takunkumin Amurka da aka ambata cikin dokar, ko da yake hakan ba zai kawar da yiwuwar Amurka ta ɗauki matakin ramuwar gayya ba.
An riga an fara ganin tasirin wannan matsala a ɓangaren inshora. A ranar 1 ga Oktoba, ICC da babban kamfanin inshora na Faransa, AXA, sun amince da dakatar da yarjejeniyar hulɗarsu.
AXA na samar wa kotun hidimomin inshorar lafiya. A cewar jaridar Financial Times, kamfanin ya ce ya ɗauki matakin ne saboda fargabar yadda Amurka za ta iya aiwatar da takunkuminta a wajen ƙasarta.
Rahotanni sun nuna cewa tattaunawar da aka shafe watanni ana yi ba ta haifar da wata yarjejeniya da za ta kare ɓangarorin biyu ba, matuƙar Turai ba ta yi amfani da dokar hana bin takunkumin ba.
Daga bisani, ICC ta samu wani kamfanin inshora da zai ci gaba da samar mata da hidimar, amma ba a bayyana sunansa ba.
Bai kamata wata kotun hukunta manyan laifuka ta ƙasa da ƙasa da ke gudanar da ayyukanta a Turai ta rasa damar samun muhimman hidimomin banki da inshora saboda rashin amincewar siyasar Washington da hukuncin da kotun ta yanke ba.
Kiraye-kirayen ɗaukar mataki na fitowa daga cikin Tarayyar Turai kanta. Mambobin Majalisar Tarayyar Turai 58 sun rubuta wa shugabar Hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen, wasiƙa bayan sabon takunkumin da aka kakaba, inda suka buƙaci a fara amfani da dokar Blocking Statute.
Majalisar ta kuma sha yin kira da a samar da irin wannan kariya a wasu kudurorinta na baya.
Waɗannan wakilai sun fahimci abin da ka iya faruwa idan aka bar wata ƙasa ta waje ta riƙa yanke shawarar ko wata hukuma da ke da hedikwata a Turai za ta iya samun hidimomin kasuwanci na yau da kullum ko a'a.
Shin Turai za ta iya tunkarar Amurka?
Duk da haka, akwai tambayoyi masu muhimmanci kan irin tasirin da dokar za ta iya yi.
A shekarar 2018, lokacin da Turai ta yi wa dokar gyara domin tunkarar sabbin takunkuman Amurka kan Iran, kamfanonin da ke da manyan harkokin kasuwanci a Amurka sun ci gaba da fargabar rasa damar shiga kasuwannin ƙasar da hanyoyin hada-hadar kuɗaɗenta.
Haramcin da dokar Turai ta sanya ba ya kawar da waɗannan haɗurra. Haka kuma, ba lallai ne ya sa babban bankin ƙasa da ƙasa ya yarda ya sadaukar da kasuwancinsa a Amurka ba.
Hukumar Tarayyar Turai tana da dalilin yin la'akari da irin waɗannan tsadar matakai, amma kasancewar hanyar magance matsalar ba cikakkiya ba ce bai kamata ya zama dalilin ƙin amfani da ita ba.
Saboda haka, ya kamata a haɗa fara amfani da dokar da wasu matakai na zahiri na kariya. Ya kamata EU ta samar da ingantattun hanyoyin biyan kuɗi ta amfani da Euro, ta yi aiki tare da bankuna da kamfanonin inshora da ke shirye su yi wa kotun hidima, tare da rage dogaro da fasahohin Amurka da ka iya zama cikin haɗari.
Haka kuma, ya kamata ta tabbatar da cewa ana aiwatar da dokar yadda ya kamata, tare da ba da cikakken bayani kan irin ayyukan da aka amince a gudanar da su da kuma waɗanda za a iya keɓancewa.
Idan ana sa ran kamfanonin Turai za su yi tsayin daka wajen ƙin amincewa da matsin lambar da ya fito daga wajen ƙasashensu, to ya kamata gwamnatocinsu su yi fiye da yaba musu kan jarumtaka, alhali suna barin su su kaɗai su ɗauki asarar da hakan zai jawo.
In ba haka ba, hakan zai haifar da wani yanayi na dogaro da wata ƙasa wajen gudanar da harkokin hukumomi. Shugabannin Turai na yawan magana kan buƙatar ƙasashensu su samu damar cin gashin kansu a dabarun hulɗa da sauran ƙasashe, da kuma tsarin duniya da doka ke tafiyarwa.
Suna sanya dokoki ga manyan kamfanonin fasahar Amurka, suna kare 'yancin kasuwannin Turai, tare da ikirarin cewa suna da nasu ra'ayi mai zaman kansa kan harkokin duniya.
Sai dai idan takunkumi ya shafi wata kotu da ke Hague, sai su koma neman Washington ta sake duba matakinta. Don haka, matsalar ba wai rashin dokokin da za su yi amfani da su ba ce, a'a, ita ce ko suna da ƙarfin siyasar da za su aiwatar da su.
Haka kuma, martabar Turai na cikin jarabawa. Gwamnatocin ƙasashen Turai sun nuna goyon baya sosai ga binciken da ICC ke yi kan zargin aikata laifuka da Rasha ta yi a Ukraine, da kuma sammacin kama Shugaban Rasha Vladimir Putin.
Bai kamata wannan goyon baya ya gushe ba lokacin da kotun ta binciki zarge-zargen da suka shafi shugabannin Isra'ila ko jami'an Amurka.
Ya kamata a tantance zarge-zargen bisa hujjoji da dokoki, ba wai bisa ƙasar da wanda ake zargi ya fito ko ƙarfin diflomasiyyar gwamnatinsa ba.
Idan aka maraba da shari'ar manyan laifuka ta ƙasa da ƙasa idan ta shafi abokan hamayya, amma aka kawo mata cikas idan ta shafi ƙawayen ƙasashe masu ƙarfi, to zai yi wuya a kare manufar cewa kowa yana daidai a gaban doka.
Wannan rashin daidaito ba ya ɓuya ga ƙasashen Afirka, Asiya da Latin Amurka, inda ake yawan korafi tun shekaru da dama kan yadda ake aiwatar da shari'ar ƙasa da ƙasa bisa zaɓen waɗanda za a hukunta.
Gwamnatoci da dama sun amince da Yarjejeniyar Rome ne bisa fahimtar cewa za a binciki manyan laifuka ba tare da nuna wa wasu gata saboda matsayinsu na siyasa ba.
Idan Turai ta ƙi kare kotun a lokacin da Washington ta nuna rashin amincewa da ayyukanta, hakan zai ƙara ƙarfafa ra'ayin cewa akwai wata keɓantacciyar doka da ba a rubuta ba da ke bai wa manyan ƙasashen Yamma kariya daga ƙa'idojin da ake cewa na kowa ne.
Ba za a iya gyara illar da bayyanannen munafunci ke haifarwa cikin sauƙi da yawan kalaman kare haƙƙin bil'adama ba.
Ya kamata Hukumar Tarayyar Turai ta yi wa ƙarin bayanan dokar Blocking Statute gyara domin ta shafi takunkumin da aka kakaba wa ICC, sannan ta yi amfani da watannin da suka rage kafin karewar lasisin Amurka wajen samar da ingantattun matakan kariya.
Haka kuma, ya kamata ta bayyana karara cewa rashin amincewa da hukuncin kotu ba ya ba kowa damar yin katsalandan ga 'yancin gudanar da ayyukanta.
Ba lallai ne Turai ta amince da dukkan hukuncin ICC ba kafin ta kare 'yancin da kotun ke da shi na yanke hukunci ba tare da fuskantar barazanar matsin lambar tattalin arziki ba.
Shin a ƙarshe Turai za ta yi amfani da ikon doka da take ikirarin tana da shi, ko kuwa za ta ci gaba da zama a matsayin wadda ke neman yardar Washington kafin ta kare ƙa'idojin da take cewa ba za ta taɓa sassautawa ba?
Amsar wannan tambaya za ta shafi alkalai a Hague da kuma waɗanda ke jiran a yi musu adalci a sassa daban-daban na duniya.
Haka kuma, za ta bayyana ko ikirarin Turai na son cin gashin kanta a harkokin dabarun siyasa da diflomasiyya da gaske take yi, ko kuwa kalma ce kawai da take yawan maimaitawa a duk lokacin da aiwatar da ita zai zama mata da wahala.
Marubuci: Ziyad Motala, Farfesa a fannin Shari'a a Makarantar Shari'a ta Jami'ar Howard da ke Washington DC. Yana koyar da dokokin ƙasa da ƙasa da kuma dokokin kundin tsarin mulki. An haife shi a Afirka ta Kudu, kuma ya taka rawa a gwagwarmayar neman 'yancin ƙasar. Ya haɗa hannu da Shugaban Afirka ta Kudu na yanzu, Cyril Ramaphosa, wajen rubuta littafin Constitutional Law, Analysis and Cases.
Bayani: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyana a wannan rubutu ba lallai ne su kasance ra'ayi ko matsayar edita ta TRT Afrika ba.












