| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Dakarun Nijeriya sun kashe mayakan DAESH 48, sun ƙwato makamai a jihohin Borno da Yobe
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Jumma’a, rundunar ta ce dakarunta sun dakile wani yunƙurin kai hari kan sansanin soji da ke Bitta, a ƙaramar hukumar Gwoza ta Jihar Borno, a daren ranar 29 ga Oktoba.
Dakarun Nijeriya sun kashe mayakan DAESH 48, sun ƙwato makamai a jihohin Borno da Yobe
Sojin Nijeriya

Dakarun sojin Nijeriya sun kashe mayakan ISWAP 48 tare da ƙwato tarin makamai da alburusai bayan dakile hare-hare da aka kai kan sansanonin soji a jihohin Borno da Yobe.

Rundunar sojin ta ce dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Gabas, ƙarƙashin shirin Operation HADIN KAI, ne suka gudanar da ayyukan tsakanin ranakun 29 da 30 ga Oktoba, 2026.

A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Jumma’a, rundunar ta ce dakarunta sun dakile wani yunƙurin kai hari kan sansanin soji da ke Bitta, a ƙaramar hukumar Gwoza ta Jihar Borno, a daren ranar 29 ga Oktoba.

Ta ce haɗin gwiwar dakarun ƙasa da tallafin jiragen yaƙi ya yi galaba a kan maharan, tare da tarwatsa shirin harin da kuma kashe da dama daga cikinsu.

A wani hari na daban, dakarun sun dakile harin da wasu gungun mayakan ISWAP suka kai kan Makarantar Horar da Sojoji ta Arewa maso Gabas (NETTS), da ke Buni Yadi, a ƙaramar hukumar Gujba ta Jihar Yobe.

A cewar rundunar, an shafe kusan sa’o’i biyar ana fafatawa, daga ranar 29 ga Oktoba zuwa safiyar ranar 30 ga watan. An gudanar da aikin ne bisa haɗin gwiwar dakarun ƙasa da na sama, tare da amfani da bayanan sirri da na’urorin sa ido da leƙen asiri.

Rundunar ta ce harin ramuwar gayya da dakarunta suka kai ya yi sanadin mutuwar mayakan 48, tare da kwato makamai da alburusai masu yawa.

Makamaman da aka kwato sun haɗa da bindigogin AK-47 guda 42, manyan bindigogin PKT guda biyar, bindigogin GPMG guda huɗu da kuma makamin harba bama-bamai mai nauyin milimita 60 guda ɗaya. Dakarun sun kuma kwato harsasai masu caji na AK-47 guda 105 da kyamarorin ɗaukar bidiyo guda biyu.

Sauran kayayyakin da aka kwato sun haɗa da harsasan makamin yaƙi da sulke guda 30, harsasan 7.62mm guda 2,738, harsasan 7.62mm NATO guda 223 da kuma harsasan PKT guda 2,054.

Rundunar ta ce an rasa soja guda ɗaya a fafatawar, yayin da wasu sojoji biyu suka samu raunuka marasa tsanani, kuma suna samun kulawar likitoci.

Ta ƙara da cewa ƙwarin gwiwar dakarunta na nan daram yayin da suke ci gaba da kai hare-hare kan ƙungiyoyin ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas.

Rundunar ta bayyana nasarorin da aka samu a matsayin babban koma-baya ga ’yan ta’addan, tana mai cewa asarar mayakansu da kwato makamansu zai rage musu ƙarfin kai hare-hare.

Kyaftin Mohammed Goni, Mukaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na Hedikwatar Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Gabas, Operation HADIN KAI, ne ya sanya hannu kan sanarwar.