| Hausa
TATTALIN ARZIKI
2 minti karatu
Ghana ta fara tattaunawa da Rasha don gina tashar makamashin nukiliya ta farko a ƙasar
Shugaban ƙasar Ghana John Dramani Mahama ya bayyana cewa Ghana ta fara tattaunawa da kamfanin makamashin nukiliya na gwamnatin Rasha, Rosatom, kan tsare-tsaren gina tashar makamashin nukiliya ta farko a ƙasar.
Ghana ta fara tattaunawa da Rasha don gina tashar makamashin nukiliya ta farko a ƙasar
Ghana ta ce tashar nukiliyar za ta samar da lantarki a matsayin cikamakon lantarki daga ruwa da kasar ke samarwa a yanzu.

Mahama ya yi wannan sanarwar ne a ranar Alhamis yayin da yake jawabi a wani babban taro tsakanin Rasha da Afirka (Russia-Africa Summit) karo na uku da aka gudanar a birnin Moscow, inda ya jaddada buƙatar samun wutar lantarki mai inganci sannan mai arha domin tallafawa harkar masana’antu a fadin nahiyar.

Shugaban na Ghana ya ce rashin wadatar wutar lantarki yana daya daga cikin manyan abubuwan da ke hana ci gaban Afirka, inda ya kara da cewa makamashin nukiliya na iya taimakawa wajen shawo kansa da biyan bukatun makamashi na nahiyar da ke karuwa.

“Mun fara tattaunawa da Rosatom game da kafa tashar makamashin nukiliya ta farko a Ghana,” in ji Mahama.

Ya bayyana cewa Ghana tana bin turbar faɗaɗa hanyoyin samun makamashi wanda ke haɗa makamashi mara gurbata muhalli (renewable energy) tare da shirye-shiryen yin amfani da makamashin nukiliya don zaman lafiya.

Wannan sanarwa ta samo asali ne a kan daɗaɗɗiyar dangantakar makamashin nukiliya tsakanin Ghana da Rasha, wadda ta samo asali tun shekarar 1964, lokacin da Tarayyar Sobiet (Soviet Union) ta samar wa Ghana injin sarrafa nukiliya (reactor) mai karfin megawatt biyu don gudanar da binciken kimiyya.

Mahama ya ce masana kimiyyar nukiliya da dama ’yankasar Ghana sun samu horo a kasar Rasha don sarrafa wannan injin.

Ghana tana ta nazarin hanyoyin amfani da makamashin nukiliya a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin faɗaɗa hanyoyin samun wutar lantarki da kuma biyan buƙatun da ke ƙaruwa sakamakon ƙaruwar jama’a da haɓakar masana’antu.

Tashar makamashin nukiliya za ta kasance tushen samun wutar lantarki ta dindindin (baseload electricity) don cika gibi da kuma bunkasa wutar lantarki da ake samarwa da ruwa kuma tsarin  turbin (thermal generation) da ƙasar ke amfani da su a yanzu.

Tattaunawar da ake yi da Rosatom tana wakiltar sabon mataki a ƙoƙarin da Ghana ke yi na gabatar da makamashin nukiliya a cikin tsarin wutar lantarkinta, kodayake ba a sanar da karshen yarjejeniya ko jadawalin lokacin gina tashar ba.

Haɗin gwiwar da ake shiri yi yana kuma nuna faɗaɗa ƙoƙarin ƙarfafa haɗin gwiwar makamashi tsakanin Rasha da ƙasashen Afirka, musamman a fannin fasahar nukiliya da makamashi mara gurbata muhalli.