An samu takun-saka tsakanin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, da Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Nijeriya (DSS), kan shirye-shiryen fara gangamin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar a Jihar Sokoto.
Shirye-shiryen gudanar da gangamin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar ADC a Jihar Sokoto sun haifar da ce-ce-ku-ce, bayan tsohon mataimakin shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin jihar da hukumar DSS da ƙoƙarin kawo cikas ga taron.
Atiku ya yi zargin cewa an shirya zanga-zangar adawa da gangamin da aka tsara gudanarwa ranar Laraba, tare da yunƙurin haddasa rikici domin hana jam’iyyar gudanar da ayyukanta na siyasa cikin walwala.
Da yake magana da manema labarai a Abuja ranar Talata, Atiku ya ce an hana ADC amfani da wasu wuraren jama’a da kuma samun masauki ga baƙin da za su halarci taron, matakin da ya bayyana a matsayin yunƙurin yi wa jam’iyyar zagon ƙasa da kuma tauye wa ’yan Nijeriya ’yancin zaɓe.
Ya kuma zargi DSS da ɗaukar nauyin wasu mutane domin gudanar da zanga-zanga da ka iya rikidewa zuwa tashin hankali, wanda daga ƙarshe zai iya zama dalilin ayyana dokar hana fita a jihar.
Atiku ya jaddada cewa aikin DSS shi ne tattara bayanan sirri da kuma taimakawa wajen kare tsaro, ba wai ƙirƙirar yanayin tashin hankali ko shiga cikin harkokin siyasar jam’iyyun ƙasar ba.
DSS ta musanta zargin, ta ce ta ceci ɗan takarar gwamna na ADC
Sai dai hukumar DSS ta yi watsi da zarge-zargen Atiku, tana mai cewa aikinta ya haɗa da kare rayukan ’yan Nijeriya ba tare da la’akari da jam’iyyarsu ta siyasa ba.
A wata sanarwa da mataimakiyar daraktar hulɗa da jama’a ta hukumar, Favour Dozie, ta fitar ranar Talata, DSS ta ce jami’anta sun taimaka wajen kuɓutar da ɗan takarar gwamnan Sokoto na ADC, Mannir Daniya, a lokacin da aka kai masa hari.
Hukumar ta ƙara da cewa jami’anta biyu da aka farmaka yayin lamarin suna jinya a asibiti.
A cewar sanarwar, Mannir Daniya da kansa ya kira daraktan DSS na jihar domin nuna godiya kan taimakon da jami’an suka bayar, tare da neman a ƙara tura jami’ai domin taimakawa wajen tabbatar da tsaro.
DSS ta kuma yi ƙoƙarin kare martabar aikinta, inda ta kawo misalin hukuncin da wata babbar kotun tarayya a Jihar Rivers ta yanke wa wani mutum mai suna Monday Udeme.
Hukumar ta ce an yanke wa Udeme hukuncin ɗaurin shekara biyu ne bayan ta gurfanar da shi kan zargin barazanar kai wa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, hari.
A cewar DSS, wannan na daga cikin misalan yadda take gudanar da ayyukanta ba tare da nuna bambanci ga jam’iyyun siyasa ba.
Duk da musanta zarge-zargen, daraktan hukumar ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan batun da Atiku ya gabatar, domin abin da hukumar ta bayyana a matsayin girmama shi a matsayinsa na dattijon ƙasa.
Sai dai ya yi gargaɗin cewa irin waɗannan zarge-zarge na iya karya gwiwar jami’an tsaro da ke gudanar da ayyukansu.
Rufe ofishin ADC ya ƙara dagula al'amura a Sokoto
Wannan takun-saka tsakanin ADC da DSS na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar ke fuskantar wata matsala a Sokoto, bayan gwamnatin jihar ta rufe ofishinta.
Gwamnatin jihar ta danganta matakin da wata takaddama kan takardun mallakar filin da aka gina ofishin a kai.
Sai dai jam’iyyar ta ce ta shawo kan matsalar, inda ta bayyana cewa magoya bayanta sun shirya ba da gidajensu domin masaukin baƙin da za su halarci gangamin.
Yayin da ake ci gaba da musayar zarge-zarge tsakanin ɓangarorin, hankalin jama’a ya karkata kan yadda za a gudanar da gangamin ADC a Sokoto, da kuma rawar da hukumomin tsaro za su taka wajen tabbatar da tsaron mahalarta taron.
Babban abin da ake jira shi ne ko jam’iyyar za ta samu damar gudanar da gangamin kamar yadda ta tsara, ba tare da tangarda ko wata matsalar tsaro ba.


















