Sakataren Majalisar Koli ta Tsaron Ƙasa ta Iran, Mohsen Rezaei, ya yi gargaɗin cewa Iran na iya kai hari kan cibiyoyin makamashi, rumbun bayanai, da ƙirƙirarriyar basira (AI) da ke da alaƙa da Amurka a ƙasashe bakwai na Yankin Tekun Fasha, idan Amurka da Isra’ila suka kai mata hari, inda ya ce ba gudu ba ja da baya, koda yake Shugaban Amurka Donald Trump ya nanata cewa ƙasarsa na iya kai wa Iran ƙarin hare-hare.
“Jijiyar tattalin arzikin Amurka a wannan yankin tana bi ta yankinmu ne na duniya,” in ji Rezaei a ranar Alhamis a lokacin wata hira da gidan talbijin na gwamnatin ƙasar mai suna Press TV, yana mai nuna manyan jarin da Amurka ta zuba a cibiyoyin bayanai da na (AI) a duk faɗin Gabas Ta Tsakiya.
Ya bayyana cewa sama da dalar Amurka triliyan 2 na kayayyakin fasaha da ke da alaƙa da Amurka a wannan yanki mai tashe-tashen hankula na iya fuskantar haɗari idan har aka ci gaba da amfani da ƙarfin soji.
“Har yanzu ba mu sanya waɗannan kayayyaki cikin wuraren da za mu iya kai wa hari ba. Amma idan yaƙi ya ɓarke, da yawa daga cikin waɗannan wayoyin sadarwa da rumbunan bayanai, wuraren cibiyoyin AI, da sauran wurare da dama za a lalata su,” in ji Rezaei.

A wata hira ta daban da kafar labarai ta Drop Site, Rezaei ya ce Iran ta gindaya sharuɗɗa bakwai ta hanyar masu shiga tsakani kuma ba za ta sake buɗe Mashigar Hormuz ba ko kuma komawa teburin tattaunawa har sai an cika waɗannan sharuɗɗa.
Ya yi gargaɗin cewa ci gaba da taƙaddama da tashen hankula a yankin na iya hana kasuwannin makamashi na duniya daidaituwa har tsawon shekaru uku.
Tasirin Yaƙin Iran Kan Zaɓukan Tsakiyar Wa’adi (Midterm election)
A halin da ake ciki, Shugaba Trump ya shaida wa manema labarai a fadar White House cewa yakin Amurka da Isra’ila da Iran ya haifar da ra’ayoyi mabanbanta a tsakanin masu jefa kuri’a na Amurka gabanin zaben tsakiyar wa’adi na watan Nuwamba, yana mai amincewa da asarar da aka tafka a siyasance yayin da yake nanata cewa an kammala kai hare-haren soji.
Yayin da yake magana kan tasirin yakin a kan zabe mai zuwa, Shugaba Trump ya bayyana cewa: “A wani bangaren, suna son shi saboda ina yin abin da ya kamata sauran shugabanni su yi, a wani bangaren kuma watakila ba sa so.
Akwai farashin da za a biya, wanda na sani nan take lokacin da na aikata hakan, amma ba za mu iya barin Iran ta mallaki makamin nukiliya ba. Ina nufin, ta wata hanyar, mutane watakila ba sa son shi, amma mutane da dama, kishin kasa na gaskiya, suna matakar son shi.”
“Wannan abu ne da ya kamata sauran shugabanni su aikata tun da dadewa. Yakin Iran, kuma mun yi musu mummunar barna, kuma za mu iya ci gaba da yi musu fiye da haka,” in ji shi.
Wadannan kalamai na nuna irin salon maganganun Trump biyo bayan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai a ranar 28 ga Fabrairu, 2026 kan wuraren hakar mai, sojoji da na nukiliya na Iran, wanda Amurka ta yi wa laƙabi da “Operation Epic Fury”.
Haren farko sun haifar da kisan Babban Jagora Ali Khamenei tare da sauran manyan jami’ai da daruruwan fararen hula.
Iran ta maida martani da jerin hare-hare ciki har wadanda ta kai da jirage marasa matuki kan Isra’ila da muradun Amurka a Yankin Tekun Fasha, tare da haifar da katsewar zirga-zirga akai-akai a Mashigar Tekun Hormuz.
Rikicin yanzu haka yana watansa na takwas.
Yarjejeniyar da aka cimma a watan Yuni a Pakistan da nufin tsayar da fada da dawo da sufurin jiragen ruwa na kasuwanci ta wargaje sakamakon sabani, wanda hakan ya haifar da ci gaba da kai hare-hare lokaci zuwa lokaci.
Farashin danye mai da sauran man fetur ya karu sosai a Amurka da sauran kasashe.
Sakamakon gudanar da binciken ra’ayoyi da aka yi a watan Oktoba ya nuna cewa goyon bayan da jama’a suke nuna wa Shugaba Trump ya ragu zuwa kashi 30–36 cikin 100, a daidai lokacin da jama’a suke nuna rashin jin dadinsu kan yadda ake tafiyar da tattalin arziki da tsadar rayuwa da kuma yakin da kasar take yi da Iran.





















