Yayin da Barcelona ta samu koma baya a wasanni biyu cikin mako guda da ta buga a baya-bayan nan, ƙungiyar ta fara neman hanyoyin faraɗowa don ci gaba da jan ragamar teburin La Liga.
Ranar 20 ga Okotba, PSG ta Faransa ta lallasa Barcelona da ci 4-2 a birnin Paris, yayin da ranar 25 ga Oktoba Real Madrid ta doke su da ci 2-1 a wasan El Clasico na gasar La Liga.
Rahotanni sun ce wannan ne ya sa tawagar ta Barca ta shirya wani ƙwarya-ƙwaryan taron ƙarfafa haɗin-kai, wanda ya samu halartar ‘yanwasan da kuma koci Hansi Flick, da ma jami’an horarwa.
Taron gasa naman ya gudana ne nesa da masu yaɗa labarai, a filin atisayen ƙungiyar na Ciutat Esportiva, da zummar ƙarfafa haɗin-kan tawagar gabanin fuskantar wasanni da ke gaba.
Yayin taron, an ambato kyaftin ɗin ƙungiyar Raphinha yana cewa ba hukumar gudanarwar ƙungiyar ce ta shirya ba. Wani yunƙuri na jagororin ‘yanwasan irinsu Rodri na yauƙaƙa dangatakar ‘yanwasan. Taron ya ɗauki kamar mintuna 90.
Ranar Asabar 31 ga Oktoba, Barcelona za ta kara da Alaves a gasar La Liga, sannan kwanaki uku bayan nan ranar 3 ga Nuwamba, su kara da Aston Villa a gasar Zakarun Turai.
















