Manyan jami’an gwamnatin Turkiyya, Saudiyya da Pakistan za su gana da jami’an Iran a Tehran don tattaunawa kan tsaron yankin, in ji jami’ai a ranar Litinin.
Ali Bagheri, mataimakin sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran, ya shaida wa gidan talabijin na Iran cewa manyan jami'ai daga Saudiyya, Pakistan da Turkiyya, mambobin kungiyar kawancen Makka, za su ziyarci Tehran a matsayin wani bangare na kokarin bunkasa tsarin tsaron yankin a Yammacin Asiya.
Bagheri ya ce taron zai samu halartar Ministan Tsaron Saudiyya Yarima Khalid bin Salman, Babban Hafsan Sojin Pakistan Asim Munir da wani babban jami'in Turkiyya.
Majiyoyin tsaron Turkiyya sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa shugaban kungiyar leken asiri ta kasa Ibrahim Kalin zai halarci taron.
Bagheri ya ce jami'an da za su ziyarci kasar za su gana da Mohsen Rezaei, sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran, domin tattauna batutuwan tsaro na yankin.
Ya kara da cewa Iran na adawa da tsoma baki da tasirin kasashen waje a yankin.
Bagheri bai bayyana ranar da za a yi taron ba, kodayake kafofin watsa labarai na Iran sun rawaito cewa zai gudana a ranar Litinin.
Kawancen Makkah na neman a sanyaya wutar rikicin ynkin
Mataimakin Ministan Harkokin Waje na Saudiyya kan Harkokin Diflomasiyyar Jama'a Rayed Krimly ya tabbatar da ziyarar a wani rubutu da ya yi a dandalin sada zumunta na X.
Krimly ya ce jami'an da suka ziyarce shi za su kuma gana da Shugaban Iran Masoud Pezeshkian, baya ga Rezaei.
Ya ce ziyarar wani bangare ne na kokarin da mambobin kungiyar Kawancen Makkah ke yi na rage tashin hankalin rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran.
Tattaunawar za ta kuma nemi bunkasa tattaunawa da lalubo hanyoyin magance matsalolin diflomasiyya yayin da take goyon bayan kokarin shiga tsakani da Qatar da Pakistan ke jagoranta, in ji shi.
Krimly ya ce masu ziyarar sun nuna rawar da mambobin kungiyar ke takawa wajen karfafa tsaro da kwanciyar hankali a yankin da kuma kudurinsu na yin aiki tare da dukkan kasashen yankin don cim ma wannan burin.
















