| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Burkina Faso za ta sauya darussan makarantu don 'kawar da tsarin mulkin mallaka' a fannin ilimi
Ministan ilimin ƙasar ya ce za su "cire kalmomin da ke bayyanamu a matsayin yara ko dabbobi, sannan mu ƙara ɗarusan da ke haɓaka al’adu da ɗabi'unmu.’’
Burkina Faso za ta sauya darussan makarantu don 'kawar da tsarin mulkin mallaka' a fannin ilimi
Burkina Faso na shirin yin gyara a darusan makarantu don 'kawar da tsarin mulkin mallaka' a karatun ɗalibai

Gwamnatin Burkina Faso ta ce ta soma yin sauye-sauye a darussan makarantu, musamman a fannin karatun tarihi da yanayin ƙasa, da kuma ilimin farar-hula a sabon zangon shekarar karatu don "kawar da tsarin mulkin mallaka" da ake koya wa ɗalibai.

"Mun yanke shawarar sake duba waɗannan darussan, da cire kalmomin da ke bayyanamu a matsayin yara ko dabbobi, tare da ƙara waɗanda ke haɓaka al’adu da ɗabi'unmu," kamar yadda Ministan Ilimi Mai Girma na ƙasar Moumouni Zoungrana ya bayyana a wani taron gwamnati da aka gudanar.

"Idan ka buɗe littattafanmu, ana nuna mu a matsayin wasu abubuwa kawai. Ba a taɓa nuna nasarorinmu ba; an fi mayar da hankali kan nuna kasawarmu da halayenmu marasa kyau," a cewar Zoungrana.

Har zuwa shekarar 1960, ƙasar Burkina Faso tana ƙarƙashin mulkin mallaka na Faransa.

Ba a yi wani sauyi a littattafan makarantunmu ba tukuna, a cewar wani malamin tarihi da yanayin ƙasa a babban birnin Ouagadougou, amma ma'aikatar ta rarraba takarda ga malamai wanda ke bayyana kalmomin da za a guje musu da kuma darussan da za a cire ko ƙara.

"Ba za mu ƙara magana game da masu bincike ba... sai dai game da mahara. Za mu gyara mayaƙan adawa na Afirka waɗanda aka nuna su a matsayin azzalumai ko kuma waɗanda ba su waye ba a cikin tsoffin littattafan karatu," in ji malamin.