| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
Messi da 'yanwasan Argentina sun mana wulakanci, "sun hana mu jesi da yin hoto", in ji kocin Benin
Tawagar Benin ta yi ƙoƙarin ribatar buga wasan bankwana da tauraron ɗanƙwallon Argentina, amma a ƙarshe an bar su hannu-rabbana duk da yunƙurin nasu, a cewar kocinsu.
Messi da 'yanwasan Argentina sun mana wulakanci, "sun hana mu jesi da yin hoto", in ji kocin Benin
Lionel Messi ya yi ritaya ne daga buga wa Argentina yana da shekaru 39 a duniya.
 

Kocin tawagar ƙasar Benin wadda ta fafata da Argentina a wasan sada-zumunta ranar Talata, ya koka kan abin da ya faru bayan wasan da aka buga a babban birnin Argentina.

Koci Gernot Rohr ya fusata game da yadda Lionel Messi, wanda ya buga wasansa na ƙarshe da tawagar Argentina, da kuma sauran taurarin Argentina suka yi na ƙin musayar jesi da ‘yanwasan Benin.

Cewar Rohr, hatta ɗaukar hoto ma an hana ‘yanwasansa yi da abokan wasansu, balle kuma da babban tauraron ƙwallo, Lionel Messi, wanda aka karrama a wasan.

Bayan wasan, Messi ya yi ritaya daga buga wa ƙasarsa yana mai shekaru 39, inda ya zura ƙwallo ɗaya ta bugun fenareti, ya kuma ba da tallafin ƙwallo biyu.

An tashi wasan Argentina tana da ci 3-0 kan Benin, abin da ya sanya Messi kammala wasa wa ƙasarsa cikin nasara da armashi.

Amma ga tawagar Benin kuwa, abin bai ƙare da daɗi ba, kasancewar bayan kammala wasan gabaɗaya an yi watsi da lamarin ‘yanwasansu.

Jiran minti 30

A cewar kocin, jami’an tsaro sun hana ‘yanwasansa gaisawa da ‘yanwasan Argentina, balle su yi musayar jesi kamar yadda aka saba gani a irin wannan wasa na biki.

Tawagar ta Benin ta yi ƙoƙarin ribatar wasan na bankwana da tauraron ɗanƙwallon, amma a ƙarshe an bar su hannu-rabbana duk da yunƙurin nasu, a cewar kocin.

"‘Yanwasana sun yi iya yinsu, amma ba su yi nasara ba. ‘Yanwasan Argentina sun ƙi ba wa ‘yanwasanmu komai, ko da ɗaukar hoto da Messi. Mun so mu yi musayar riguna, amma ba mu samu ko ɗaya ba. Sun ma hana mu shiga inda suke,” in ji Rohr.

Rohr ya ƙara da cewa, “‘Yanwasan Argentina ba su ba ‘yanwasanmu komai ba, ko da hoto da Messi. Mun so mu yi musayar jesi, amma ba mu samu komai ba”.

Rohr ya ce shi kansa ya yi jiran minti 30 kafin daga baya kocin Argentina, Lionel Scaloni ya ba shi wata ‘yar kyauta ta tsohuwar rigar da Messi ya saka a wani wasa, wadda shi kocin ya zo da ita.

Rumbun Labarai
Portugal ta shirya karramawar bazata ga Ronaldo, ‘yanwasan za su fito da riga mai lamba 7
Pochettino ya fashe da kuka bayan amsa tayin zama kocin Manchester United
Ronaldo zai fara siris fim kan kwallo, zai fito a jarumi tare da mawaki mai tsatson Nijeriya
Tsohon shugaban FIFA, Joseph Blatter, ya kira Infantino da "mahaukaci"
Pochettino ya shirya zama kocin Manchester United, idan aka sallami Michael Carrick
Nijar ta tabbatar wa CAF shirinta na neman karɓar baƙuncin AFCON 2032 tare da Mali da Burkina Faso
Raul Gonzalez ya zama kocin ƙwararru a karon farko, ya karɓi ragamar Real Oviedo ta Sifaniya
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Portugal ta ƙi amincewa da ritayar Cristiano Ronaldo ba tare da karramawa ba
Hukumar ƙwallon Sifaniya ta soke wasannin Copa del Rey bayan mutuwar ɗanwasan da ya yi karo da gola
Kocin Man United ya ce ya san me yake yi duk da rashin tagomashin da kungiyar ke fama da shi
Jay-Z zai tura karamin yaron nan dan-baiwa a kwallo, Nevada Pierre zuwa makarantar kwallo a Sifaniya
Koci da 'yanwasan Barcelona sun yi taron gasa nama don farfadowa daga shan kaye sau biyu a jere
Yamal: Sarkin Kambin 'Kopa' da bai yi nasarar lashe Ballon d'Or ba
Harry Kane ya zama ɗanwasan Ingila na farko da ya lashe kyautar Ballon d’Or ta maza a shekaru 25
An dakatar da Cristiano Ronaldo na tsawon kwana 30 da cin sa tarar €255 kan barin sansanin Portugal
Istanbul ta cika da ɗoki da karsashi gabanin wasan Galatasaray da Barcelona a Gasar Zakarun Turai
Hukumar ƙwallon ƙafar Portugal ta dakatar da Ronaldo daga buga wa ƙungiyar ƙasar wasa
Arda Guler ya tsawaita kwantiraginsa da Real Madrid zuwa 2031
Ronaldo zai iya komawa tawagar Portugal idan yana so, in ji kocin ƙasar
Tirkashi: Real Madrid na so a ƙwace wa Barcelona kofuna 9, ta gabatar da ƙorafi mai shafi 50,000