Babbar Kotun Tarayya a Kaduna ta dage sauraren bukatar neman beli da tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasil El Rufai ya shigar zuwa ranar 14 ga Afrilu.
Alkalin kotun Rilwanu Aikawa ya sanar da ranar bayan sauraron muhawara daga bangaren da ke kara da bangaren da ke kare kansa a ranar Laraba.
Hukumar Yaki da Rashawa Mai Zaman Kanta ICPC ce ta gurfanar da El Rufai a gaban kotu bisa zarginsa da laifuka 10 da suka shafi mallake kadarorin gwamnati da almundahar kudade.
Ya musanta aikata dukkan zarge-zargen da aka yi masa.
Kotun bayar da umarnin ya ci gaba da kasancewa karkashin kulawar ICPC har sai bayan an saurari bukatarsa ta neman beli a ranar da kotun ta sanya.
Tsohon gwamnan ya isa harabar kotun da misalin karfe 9:00am a mota baka kirar Hilux inda ya samu rakiyar jami’an Hukumar DSS.
Da yake zanta wa da ‘yan jaridu bayan zaman kotun, daya daga cikin lauyoyin El Rufai, Ubong Akpan SAN ya tabbatar da dage karar amma ya ce shugaban tawaharsu zai zanta da manema labarai daga baya.
















